Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Isra'ila ta sake kai harin kisan gilla a Beirut bisa haɗin gwiwa tare da Amurka. Gwamnatin sahyoniyawan ta sanar da cewa, ta kai hari kan babban birnin kasar Lebanon a wannan harin tare sanar da Amurka. Ma'aikatar rediyo da talabijin ta Isra'ila ta nakalto wani jami'in gwamnatin kasar yana cewa: An kai harin da aka kai wa birnin Beirut tare da hadin gwiwa da Amurka.
Jiragen yakin sojin Isra'ila sun kai hari a yankunan da ke kudancin birnin Beirut. Akwai yiwuwar an hari wani kwamandan sojojin Ridwan ne na Hizbullah da mataimakansa.
Your Comment